Saturday 8 July 2017

WhatsApp Chat with مسألة إسلامية (س- و -ج)b

7/8/17, 11:24 AM - ‪+234 703 959 7838‬: *Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 2,391*
..
Cikin Ramadanne, sai na yi brush bayan alfijir ya fito, bisa kuskure, sai naji kamar na hadiyi zakin Toothpaste din, to don Allah Malam ya matsayin azumi na.

……

Amsa


_Azuminka yananan lafiya qalau tangaran babu abinda ya sameshi insha Allahu, domin mai na goge baki baya karya azumi abisa zancenda yafi inganci, hukuncinsa daya da itacen aswaki danye ko busashshe*****_


Allah yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس التعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
7/8/17, 12:53 PM - ‪+234 703 071 4263‬: *أشهر سبع مقولات للشيخ الشعراوي:*

١ 📒 إن لم تستطع قول الحق فلا تصفق للباطل.
٢ 📒 إذا لم تجد لك حاقداً فاعلم أنك إنسان فاشل.
٣ 📒 لا تقلق من تدابير البشر فأقصى ما يستطيعون هو تنفيذ إرادة الله.
٤ 📒 لن يحكم أحد فى ملك الله إلا بما أراد الله.
٥ 📒 لا تعبدوا الله ليعطي، بل اعبدوه ليرضى، فإن رضي أدهشكم بعطائه.
٦ 📒 إذا رأيت فقيراً فى بلاد المسلمين؛ فاعلم أن هناك غنياً سرق ماله.
٧ 📒 لا يقلق من كان له أب.. فكيف يقلق من كان له رب.

🌾اسعد الله أوقاتكم 🌾
7/8/17, 1:17 PM - ‪+234 818 250 8394‬: Please don't take Fanta, coke or sprite after taking vitamin C. it will be instant death. Beware, this is not a social media news but a national network news. SHARE AND SAVE LIVE.

(Sent to me and I owe my fellow human an obligation to save their lives. Please be cautious.)

http://pulse.ng/health/health-warning-taking-vitamin-c-with-fanta-or-sprite-is-dangerous-id6367508.html
7/8/17, 2:21 PM - ‪+234 703 959 7838‬: *Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 2,392*
..
Ina azumin sittu shauwal ne kuma inaso inyishi ajere, toh zan iya azumtar ranar Juma'a??
Dan naji ance ba a azumi ranar Juma'a idan ba Ramadan bane.

……

Amsa


_Eh, zaka iya, domin ita juma'a haramcin azuminta yanada sauqima ba kamar na Asabar ba, domin ita juma'a kan malamai ya hadu akan cewa kana iya hadata da Alhamis, wato idan kayi azumin ranar alhamis to babu laifi kaqarayi ranar juma'a*****_
_Amma inda rigimar take shine ko ana iya hada juma'a da asabar???_
_Ananne malamai sukayi sa6ani akwai irinsu Nasirudden Albani wayanda suke ganin cewa kwata kwata ba,a yin azumin nafila a ranar asabar saboda wani hadisi wanda Tirmizy da Abu Dawuda suka ruwaito duk da cewa hadisin yasha maganganu awajen malamai***_
_Amma abinda malamai sukafi rinjayarwa shine ana iya hada juma'a da Asabar saboda hadisin ummu salamah wabda bukhari da Muslim suka ruwaito*****_
_Sannan kuma babu kaifi a hade asabar da lahadi suma ayisu a jere, wannan shine zancenda yafi inganci Insha Allahu*****_


Allah yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس التعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
7/8/17, 2:22 PM - ‪+234 703 959 7838‬: *Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 2,393*
..
Meye hukuncin masu yada irin wadannan post din?
Dama ana fadin innalillahi wa inna ilaihin rajiun ga abin alkhairi ko farinci..?

……

Amsa


_To wannan alamace datake nuna jahilcin mutane da kuma fasiqanci, waisu ahakan gani sukeyi wai wasa suke, saboda basusan irin girman zunubinda yake cikin wasa da Ayoyin Allah ba****_
_Wanda abune dayake sananne awajen musulmi cewa idan wani musiba ta aukowa musulmi nagari shine yake fadin Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, aduk sanda wata musiba ta sameshi, kamar yadda Allah ya labarta mana acikin Suratul baqara*****_
_To shine akasamu wasu shedanun mutane a wannan zamanin sukuma se suka mayarda wannan kalma wacce ayar qur'anice seta zame musu abin wasa wai susu turo maka ita, aqasabta kuma sesu fadi wani abin Alheri ko abin ban dariya, kuma waisu aganinsu wasa sukeyi****_
_Karanta Suratul ma'ida da suratu Tauba zakaji irin narkon azaba da Allah yayi alqawari ga wayanda suke wasa da ayoyinsa, bayaga cewama da yayi a kauda kai daga garesu duk sanda kagansu****_
```Allah madaukakin Sarki ya tsaremu```


Allah yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس التعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
7/8/17, 2:22 PM - ‪+234 703 959 7838‬: *Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 2,394*
..
Menene inganchin maganar da wasu suke fada chewa idan mutum mahaifinshi ya rassu toh iyayenshi da suke chikin takaba wai idan zasu fita takaba dole sai anyi musu sabon dinki, dan Allah malam menene inganchin hakan a addinanche?

……

Amsa


_To wannan duk tatsuniya ce kawai, basuda dalili A littafin Allah ko Sunnar Annabi Muhammad (s.a.w) dan haka, se kuyi musu watsi da qaryarsu, amma babu inda akace ayi wani sabon dinki saboda za,a fita daga takaba wannan qaryace zunzurutu****_


Allah yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس التعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
7/8/17, 2:22 PM - ‪+234 703 959 7838‬: *Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 2,395*
..
Idan shafa'i da wutiri suka kufcewa mutum Shin zai iya ramawa?

……

Amsa


_To yanada kyau mutane su fahimta cewa Sha'i daban fa witry daban, kowannensu gashin kanshi yake ci****_
_Shafa'i sune raka'a biyunda akeyi bayan sallar isha'i, yayinda witri kuma shine akeso yazama sallar mutum ta qarshe acikin kowanne dare, da gwargadon yawan raka'oin, kodai raka'a daya, ko uku ko biyar ko bakwai ko tara ko sha daya*****_
_To wannan witrin shine idan mutum yasaba dama yanayinsa duk dare to idan watarana aka samu akasi bakasamu kayiba acikin daren to babu laifi kana iya ramashi a lokacin hantsi wato dai dai lokacinda akeyin sallar walaha, ammafa dole raka'a 12 zakayi, inzaka rama witri da safe to raka'oi 12 zakayi****_
Aduba *RIYADUS SALIHIN*


Allah yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس التعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
7/8/17, 2:22 PM - ‪+234 703 959 7838‬: *Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 2,396*
..
Wanda yasamu rakaa karshe asallal isha idan yamike zakaranta fatya kadai ko fatiya da sura zai karanta

……

Amsa


_Fatiha kadai ze karanta a 6oye domin cikawa akace yayi ba ramawa ba*****_


Allah yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس التعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-152200029806Y7561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
7/8/17, 2:23 PM - ‪+234 703 959 7838‬: *Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 2,397*
..
Game da musulmin da ya kashe kanshi meye hukuncin shi. Dannaji wasu suna cewa wuta ze shiga direct, kuma suna kafa hujja da wani wanda manzan Allah yace dan wuta ne, saboda ana yaki wannan mutumin yanata kashe kafirai daga karshe anci galaba za'a kashe shi se ya kashe kansa

……

Amsa


_Toh mutuminda ya kashe kansa da gangar, inhar ya aikata hakanne kuma yaname halastawa, wato yahalastawa kanshi cewa halasne ya kashe kanshi kuma ya kashe kanshi din to wannan zeshiga wutar jahannama kuma ze dauwama acikinta babu ranarda ze fita daga cikinta, Allah ta'ala ya tsaremu****_
_Amma idan yakashe kan nashi kuma yanada yaqinin cewa hakanfa ba halas bane, wato ya tabbatarda cewa haramunne a gareshi ya kashe kanshi amma zuciya da shedan sukafi qarfinsa har ya kashe kan nashi to wannan shikuma hukuncinsa yana wajen Allah, idan yaso yana iya yafe masa ba tareda yayi masa wata uquba ba, in kuma yaso seya sakashi a wuta na wani lokaci amma dai baze dauwama acikin wutarba******_
```Allah madaukakin sarki ya tsaremu```


Allah yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس التعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-152200029806Y7561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
7/8/17, 2:23 PM - ‪+234 703 959 7838‬: *★ALKAKI DA RUWAN ZUMA★*

_Ingantaccen Tarihin Sayyadi Rasulilahi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wassalam_

_(FItowa ta 10)_


Me Ya Sa Aka Zabi Yankin
Larabawa;»»»

6. Yaren da suke amfani da shi; larabci
shi ne wanda Allah a cikin hikimarsa
ya sanya shi ya zamo yaren da za a isar
da sakonsa na karshe da shi.

Alkur'ani
a matsayinsa na gamammen sako zuwa
ga duniya mai jama'a iri daban daban
da miliyoyin harsuna da dabi'u, wanda
kuma zai wanzu har zuwa tashin
kiyama yana bukatar harshe mai fadi
tare da sauki da fasaha da kuma
gwaninta wajen bayyana abinda ake so
zuwa ga mutane.

Masana sun tabbatar
larabci shi kadai ke da wannan kamala.


Bari mu dan yi wani kwatance a nan
tsakanin harshen larabci da kuma na
nasara (turanci) wanda a duniyar yau
yake cin karensa ba babbaka a
matsayinsa na yare mai daraja ta daya
a idon duniya.

Idan ka dauki wadannan
kalmomi na lamirin abokan magana
guda biyar a larabce, su ne: Anta, Anti,
Antuma, Antumu da kuma Antunna.
Ba wata fassarar da zaka iya ba su da
turanci sai "You". Tun daga nan ka ga
fasahar ba ta zamo daya ba.


A kan
haka ne cikin hikimar madaukakin
sarki ya zabi wannan kammalallen yare
don isar da mafi cikar sakonsa a
hannun mafi cikar mutane zuwa ga
al'umma mafificiya.
Wannan shi ne dalili na karshe da
zamu iya kawowa domin nuna hikimar
da ke cikin tada manzonmu na karshe a
wancan yanki na duniya da ake ganin
sa a matsayin mafi ci baya a duniyar
wancan lokaci.

Babu shakka, Allah (T)
ya yi babbar ni'ima ga wadannan bayi
nasa; larabawa da ya dora ma su
wannan gagarumin aiki.

Suna a cikin
halin rauni sai ya karfafa su.

Suna
jahilai ya ilmantar da su. Suna
talakawa ya wadata su. Suna a tarwatse
ya hada kansu. Suna a matsayin sifili a
cikin duniya ya mayar da su su ne
kowa, albarkancin farin jakadan da
muke haramar shiga cikin cikin
tarihinsa mai tsarki, wanda suka zamo
baradensa.

Take wadannan bayin Allah
da aka zaba suka rufa masa baya, suka
kulla adawa da duk wanda ya yi fatali
da kiransa.

Suka kawar da manyan
daulolin da ke hada-hada a wancan
lokaci cikin yan shekaru kadan.

A
hankali sai addinin musulunci ya game
duniya baki daya.

Don haka, daga cikin manyan darussan
wannan tarihi da zamu karanta akwai
koya mana mutuntawa da kauna da
kyakkyawar addu'a ga magabatan
wannan al'umma nagartacciya.

Kamar
yadda madaukakin sarki ya karantar da
mu bayan da ya kawo labarinsu, in da
yake cewa:

( ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺟﺎﺅﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﺭﺑﻨﺎ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻨﺎ
ﻭﻹﺧﻮﺍﻧﻨﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺳﺒﻘﻮﻧﺎ ﺑﺎﻹﻳﻤﺎﻥ ﻭﻻ ﺗﺠﻌﻞ ﻓﻲ
ﻗﻠﻮﺑﻨﺎ ﻏﻼ ﻟﻠﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﺭﺑﻨﺎ ﺇﻧﻚ ﺭﺅﻭﻑ ﺭﺣﻴﻢ )

Ma'ana: "Kuma da wadanda suka zo a
bayan su suna cewa, ya ubangijinmu!

Ka gafarta mana kuma da yan uwanmu
da suka riga mu ba da gaskiya. Kuma
kada ka sanya jin haushi a cikin
zukatanmu ga wadanda suka yi imani.

Ya ubangijinmu! Hakika, kai ne mai
tausayi, mai jinkai".

Suratul Hashr: 10.
Mu kwana lafiya yan uwana.

Mu hadu a fitowa ta gaba......

Rubutawa :- Dr, Mansur Sokoto

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑_*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
7/8/17, 2:23 PM - ‪+234 9075348806‬: NASIHA
Daure kayi biyayya ga iyayenka domin watarana kaima mahaifine
7/8/17, 2:23 PM - ‪+234 9075348806‬: NASIHA
Rike karatun qur'ani domin watarana zai ceto agareka
7/8/17, 2:23 PM - ‪+234 9075348806‬: NASIHA
Yi bautar allah kamar kana ganinsa saboda shi yana ganinka
7/8/17, 3:02 PM - ‪+234 813 232 5256‬: Jxk
7/8/17, 6:24 PM - ‪+234 813 232 5256‬: Idan ka zamanto Mutumin kirki,mai kyakkyawar manufa a rayuwa, sai Allah ya hadaka da mutanen kirki masu kyawawan manufofi irin naka, domin samun cikar burinka.

Koda ka samu matsala da wani daga cikin Jama'arka, kar ka fidda tsammanin alkhairi daga gareshi. Watakil idan kayi masa uzuri ka kyautata zato gareshi, ka yafe masa, sai alkhairi ya biyo bayan hakan.

Mutanen kirki anan duniya, sune ma'abotan alkhairi a lahira. Kuma mutum ba ya zama mutumin kirki har sai tunaninsa da ayyukansa duk sun zama na kirki.

Kayi kokari ka chanza rayuwar wani bawan Allah daga mummuna zuwa kyakkyawa. Ko ta hanyar shawarwari, ko taimako, ko agaji, ko kuma ta dalilin afuwarka.

Allah shi bamu dacewa aduniya da lahira. Ameen
7/8/17, 7:28 PM - ‪+234 806 169 6819‬: Dan Allah ina bukatar sharhi sosaii akan wannan tambayar
7/8/17, 8:37 PM - ‪+234 813 232 5256‬: A kullum zakaji ance wane ya mutu,wance ta mutu kaikuma gaka kananan a raye, tunaninka zaice 'su sun mutu nikuwa ganinan ban mutuba' kanajin dadi to suma kwanakinsune yakare. Kaima naka kullum raguwa sukeyi, kataba tunanin kwana nawa ya rage maka?
7/8/17, 8:37 PM - ‪+234 813 232 5256‬: Ya jamaa mu zauna Lafiya da junanmu. Duniya ba gurin zama bane. Bazamu dawwamaba. Duk wanda ka zalunta da harshenka koda hannun ka to Allah zai saka masa.
7/8/17, 8:37 PM - ‪+234 813 232 5256‬: Mutuwa bata sallama idan zatazo bakasan awanne hali zata riskekaba,shiyasa akeson mutum koyaushe ya kasance cikin aikata alkhairi.
7/8/17, 8:37 PM - ‪+234 813 232 5256‬: Harshe shine babban abinda ke kai mutum ga halaka,shiyasa manxon Allah sallallahu alaihi wasallam yace kafadi alkhairi ko kayi shiru.
7/8/17, 8:57 PM - ‪+234 703 959 7838‬: _*ZABURARWA AKAN YIN AURE*_

*FITOWA TA 1*

*zaburar Da Matasa akan yin Aure akan Kari*
_Allah SWT ya Sanya aure atsakanin jinsi biyu Kuma ya halicci Mutane yasan ya aure atsakaninsu ta hanyar halittar Namiji da Mace,Sunnah ce ta Annabawa da Manzanni kamar yadda yazo cikin Suratul Ra'ad Aya ta 38,Ya Shar'anta aure cikin Suratun Nisa'i Aya ta 3, Dan haka aure muhimmin Abu ne cikin tafiyar da rayuwa ta al'umma_
-Allah ya kwadaitar damu da yin aure cikin Suratun Nur aya ta 32 yace *Ku aurar da wadanda basu da aure maza da wadanda basu da aure Daga cikin ku mata da salihai Daga cikin bayinku maza da Mata idan sun kasance talakawa ne faqirai Allah zai azurta su Daga falalar shi Allah yalwatacce ne GA buqatun bayinshi Kuma masani* aqarqashin wannan Aya An ruwaito Daga Ibn Abi Haatim Daga said Dan Abdulaziz Yace ya riskeni cewar Lallai Abubakar RA yace *Kuyiwa Allah da'a cikin abin da ya umarceku na Daga aure sai ya cika maku alqawarin da yayi maku na wadata saboda fadin Allah cikin wannan a yar*_Dan haka duk of Wanda yace maka/maki cikin aure akwai talauci to ya sabawa koyarwar Alqur'ani da hadisai acikin wani hadisi Na Nana Aisha Allah yaqara Mata yarda Wanda hadisi ne Hassan Acikin Sahihu sunanu ibn Maajah 1508, Annabi Saw yace Aure Na Daga cikin sunnah ta Wanda baiyi aiki da sunnah ta ba baya tare dani,Kuyi aure domin Inkasance mafi yawan al'umma gobe alqiyama Wanda yasamu iko yayi aure Wanda bai samu ba yayi azumi domin shi garkuwa ne (Daga shaawa)_

_Imamu Ahmad yace: *Duk Wanda yakirayeka/ki akan kada kayi aure to ya kirayeka/ki zuwa GA wanin addinin musulunci* wa'iyazu billah shiyasa a wani hadisi na Dan Abbas yace Manzon Allah SAW ya kasance Yana cewa babu yankewar aure a musulunci_

_Iyaye Maza da Mata me yake sanyaku kawar da Kai Daga umarnin Allah da amanar da Allah ya baku da bada gudunmawa wajen qaruwar zinace Zinace da taushe haqqin yayanku,_

Zamu ji wasu Daga cikin faidoji na aure da wuri da illar kyamatarshi

Dan'uwanku: *Hassan M. Yandoma Abu Ammar*

*ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
7/8/17, 9:13 PM - ‪+234 803 132 3848‬: Wasu daga cikin 'Yan Matan Yau Zasu Baka Mamaki Sosai Idan Ka Kalli Yadda Suke Gudanar Da Rayuwarsū; Zaka Gansu Da Handset Mai Tsada Irinsu; Iphone6 Ko 6plus; Galaxīes, Blackberries Just Saboda Kawai Kada Aji Kunya Wajen Guys.
Babban mamakin kuma shine Idan Ka Kalli Handset Din Zaka Ganta a Rufe Kirif Da Phone-Cover, Ga Guidance Series An Zagaye Wåyar Da Shi.
Idan Ka Kalli Screen 'Din Zaka Ga An Sanya Masa Screen Guard Mai Tsada Unbreakable.
Idan Kaga Keys Din, An Basu Kariya Da Keypad-Protector.
Amma Inda Gizo Ke Sakan Kuma Abin Haushin Shi Ne: Suna Tafiya Akan Hanya Duk Jiki a Waje Babu Protection Ko Kuma Cover WHY???
Shin Wayarku Tafi Ku Daraja Kenan Ko Kuma Baku San Mutuncinku a Matsayinku Na Mata Bane???
Kuna Tafiya Da Kaya 'Damammu Transparent Just Kawai Don Ku Ja Hankaln Wasu.
ALLAH Shi Kyauta, Ya Shirye Mu Baki Daya Ameeen.
7/8/17, 9:54 PM - ‪+234 703 959 7838‬: *```Assalamu alaikum```*

*```Malam ina tambaya ne akan tsawon shekara nawa ciki yakeyi a mahaifa? Nagode```*


_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


A wannan matsalar akwai ra'ayin malamai da dama, haka Kuma a gefe daya akwai ra'ayin likitoci.


A fagen malamai akwai ra'ayi da dama akan tsawon lokacin da mace ke zama da ciki kafin ta haife shi. Akwai zantuttuka kanar haka:

1. Mafi tsawon lokaci shine: lokaci da aka saba dashi. Wato shine wata tara (9months). Wannan shine fadar _*As-haabu Mazhaba Zhahariy.*_

2. Mafi tsawon lokacin zaman Ciki shine shekara daya. Wannan shine fadar _*Muhammad ibn Abdulhakam,*_ kuma shine zabin _*Ibn Rashad.*_

3. Mafi tsawon lokacin ciki zuwa haihuwarsa shekaru biyu ne. Wannan fadar _*Mazhabar Hanafiyyah.*_

4. Mafi tsawon lokacin Ciki zuwa haihuwarsa shine: shekaru uku. Wannan shine fadar _*Lais bin Sa'ad.*_

5. Mafi tsawon lokacin ciki zuwa haihuwarsa shine: shekaru hudu. Wannan fadar a wajen _*Mazhabar Shafi'iyyah da Hanabilah,*_ a wajen _*Malikiyyah*_ zance biyi ne, wasu sunce: shekaru hudu da 'yan watanni.

6. Mafi tsawon lokacin ciki zuwa haihuwarsa shekaru biyar ne. Wannan ruwaya ce Daga _*Imam Malik.*_

7. Tsawon lokacin ciki zuwa haihuwarsa shekaru shida ne, wannan ruwaya ce daga _*Zahariy da Malik.*_

8. Mafi tsawon shekarun da ciki zai iya dauka zuwa haihuwarsa shine: Shekaru bakwai ne. Wannan shine fadar _*Rabii'atul Ra'ayi*_ kuma ita wata ruwaya ce daga _*Zahriy da Malik.*_

9. Babu tsayayyen adadin lokacin da ciki yake dauka zuwa haife shi. Wannan shine qaulin _*Abu Ubaida da Shaukaani da Bin Bazz da Ibn Uthaimin.*_

*DUBA:*
_*(Al-Mahliy Na Ibn Hazam, 10/316),*_
_*(Al-Mughni Na Ibn Qudaamah, 9/116),*_
_*(Adwa'ul Bayaan, 2/227).*_


A bangaren likitoci sunyi sabani a zantuka guda uku.

1. Wata goma (10months).

2. Kwanaki 310.

3. Kwanaki 330.


Amma abinda lafiya yawan masu bincike Na zamani suka zaba shine, mafi tsawon lokacin cikin mace zuwa haihuwarsa shine abinda ke tsakanin watanni Tara zuwa shekara daya (9months ---- 1year).
Wannan shine qaulin *Ibn Abdul-Hakam* da kuma *Ibn Rashad* (rahimahumallah). Kuma wannan qaulin baida tazara sosai da qaulin likitoci.




والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑_*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
7/8/17, 9:54 PM - ‪+234 703 959 7838‬: *_MIJINA BA YA SALLAH, KO ZAN IYA NEMAN YA SAKE NI???_*


*Tambaya:*
Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya kara basira, malam wata mata ce take son a fada mata hukuncin zama da mijinta da bai damu da sallah ba, ko da kuwa lokacin Ramdahana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana saduwa da ita tana jinin haila, kuma ta fada masa haramun ne amma ya ki ya daina, shin malam za ta iya neman saki tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama da shi? , na gode Allah ya karawa malam basira da hazaka.


*Amsa*
Wa'alaikum assalam To 'yar'uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki iya neman saki, saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a zance mafi inganci, kamar yadda Annabi S.A.W ya fada a hadisin da Muslim ya rawaito mai lamba ta: 81.

Ga shi kuma aya: 10 a suratul Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin musulma ga kafiri, kin ga cigaba da zamanku akwai matsala a addinan ce.

Allah ya hana saduwa da mace mai haila a suratul Bakara aya ta: 222, Saduwa da mace da rana a Ramadhana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 616 ya tabbatar da hakan.

Saidai zunubin barin sallah shi kadai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki ba, za ki iya kai shi kotu, alkali ya raba ku.

Don neman Karin bayani duba Al-minhajj na Nawawy 2\69.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑_*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
7/8/17, 10:14 PM - ‪+234 703 000 6494‬: Amin

Chat history is attached as "WhatsApp Chat with مسألة إسلامية (س- و  -ج)b.txt" file to this email.

No comments:

Post a Comment