Sunday 9 July 2017

خزام


YA ALLAH KA SHIRYE MU CIKIN DUKKAN LAMARIN MU , DAGA NAN JOS HAR RISHI A WATAN JULY DIN NAN BABU KALENDAR DUNIYA DA AKA YARDA DA ITA KO WANI AGOGON QWARAI MAI QA'IMAR LOKUTAN SALLAH DA YA NUNA ISHA'I NA YI QARFE 8 NA DARE, SAI TA WUCE LOKACIN ISHA YA KE YI A JULY DIN NAN SAN NAN SAI LOKACI YA YI A KIRA SALLAH, SANNAN IN AN KIRA SALLAH A SAURARA GWARGWADON DA MASU BI ZA SU YI CIKAKKEN TSARKI DA ALWALLA KA GA AQLLA MINTI 10, SANNAN IQAMA, AMMA SON ZUCIYA NE? KO JAHILCI NE? KO SAKACI NE? KO WANI 6OYAYYEN ILMI NE? WAI WASU MALAMAI SUN ZAUNA SUN GANO ISHA NA YI BAYAN AWA DAYA DAGA YIN MAGRIBA, WANDA IN KA DUBA FATAWAR LAJNAH DÃ'IMA SUN CE BA SA TAMMANIN AKWAI WANI WAJE A DUNIYAR NAN DA SA'A GUDA BAYAN MAGHRIBA ZA TA ISA A YI ISHA, KO ZAMA DA ENSHIAH NE? KO MEYE? WANNE SAURI AKE YI, DA YAWA MA MASU KURIN BIN WADANCAN MALAMAN BA SU CIKA AWA 1n BAYAN MAGHRIBA SAI KA JI ANA ISHA, YA ALLAH KA FAHIMTAR KA KUMA DORA MU KAN DAEDAI, KA KAARE MU DAGA ASARAR AIKI, DA AIKIN DA-NA-SANI.

شدة الشبه من الشيء - المعارض

No comments:

Post a Comment