ya kamata ku mana uziri, ku abin da kuke fahimta ba daidai ba ne, mu ba mu gane hakan ba, kuma da ma can abin da ya raba tafiyar ke nan, akwai abin da ya haɗa mu, kuma akwai inda in ana son zama lafiya a bar kowa da fahimtar sa, ko kuma ka wayar min da kai, in ka ga ban gane ba, kafin ka zarge ni da rashin fahimta ya kamata ka zargi kan ka da rashi iya karantarwa.
jefaffeniya ba ta haihuwar ɗa mai ido, kuma zamba ko zagi ko ashar ba fa sadaukar da kai ko lokaci ake a koye su ba, kuma za ka yarda da ni idan nace maka ni da kai mun yi ittifaqi kan cewa:( yarfe, zamba, zagi ko muzantawa) ba ɗabi'ar ƙwarai ba ce.
ALLAH MUKE ROƘO YA TSARSHE MU SHARRIN SON ZUCIYA DA NA AIKI DA JAHILCI.
11:46PM Tue, May 16.
Abdu Bello Rishi
No comments:
Post a Comment